Wani rahoton da Bankin Duniya ya fitar ya nuna cewa, an yi hasashen tattalin arzikin kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara zai karu daga kashi 2.5% a shekarar 2018, zuwa kashi 2.6% a shekarar 2019.

A rahoton bankin game da tattalin arzikin Afrika karo na 20, ya nuna cewa, matsayin bunkasar tattalin arzikin yankin a shekarar 2019 bai taka wata rawar a zo a gani ba sakamakon matsalolin rashin tabbas game da makomar tattalin arzikin duniya, da kuma tafiyar hawainiyar da ake samu wajen aiwatar da muhimman gyare-gyaren da za su bunkasa tattalin arzikin shiyyar.

Binciken ya bayyana cewa, shirin bunkasa sana'o'in dogaro da kai na mata wani muhimmin al'amari ne ga ci gaban dukkan al'ummar kasashen Afrika.

Yankin Afrika dake kudu da Sahara shi ne kadai yanki a fadin duniya wanda zai iya karfafawa mata gwiwa wajen samun sana'o'in dogaro da kai sama da takwarorinsu maza, a cewar rahoton.