Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana yunkurin tsige shi da ‘yan majalisar wakilan kasar ke yi da cewa, yunkurin juyin mulki ne.

A cikin wani bayani da ya saka a shafinsa na twitter, Donald Trump ya bayyana cewa; abin da yake faruwa na yunkurin tsige shi, ya fahimci cewa yunkuri ne na neman yi masa juyin mulki.

Ya ce masu neman tsige shi suna neman mulki ne kawai, suna son haramta wa al’ummar Amurka ‘yancin da Allah ya ba su da kuri’arsu.

Tun a ranar 25 ga watan Yulin da ya gabata ne dai wani jami’in hukumar leken asirin kasar Amurka ya fallasa wasu maganganu na sirri da suka gudana tsakanin Trump da shugaban kasar Ukraine.

Wannan batu ya sanya ‘yan majalisar wakilan Amurka suka bukaci daa gudanar da bincike kan wannan batu, musamman ma zargin da ake yi cewa maganganun, inda ake zargin cewa Trump yana neman shigo da wasu bangarori daga waje a cikin harkokin zaben kasar, wanda hakan ya sabawa dokar kasar Amurka.

Yanzu haka dai majalisar wakilan kasar ta Amurka tana shirin gayyato Trump domin ya bayyana a gabanta domin ya amsa tambayoyi, wanda kuma tabbatar da wannan laifi a kansa na iya kaiwa ga tsige shi daga kan shugabancin Amurka.