Ofishin fira ministan kasar Tunusiya ya sanar da sauke ministocin harakokin waje da na tsaro bayan shawara da shugaban kasar.

Kamfanin dillancin labaran Tunus Al-Ifrikiya ya ruwaito ofishin fira ministan kasar a jiya talata na cewa daga ranar 30 ga watan Oktoba, gwamnati ta dakatar da ministan tsaron kasar Abdul-karim Al-zubaidi tare da maye gurbinsa da ministan shari'a na kasar Karim Al-jamusi.

Har ila yau sanarwa ta kara da cewa an sauke Khamis Al-juhainawy ministan harakokin wajen kasar tare da maye gurbinsa da mataimakinsa Sabry Bashatbaji.

Sanarwar ta ce kafin daukan wannan mataki,saidai ofishin fira ministan kasar ya yi shawara da sabon shugaba kasar Kais Sa'ied.

Kais Saied dan takara mai zaman kansa shi ne ya samu nasarar lashe zaben kasar Tunusiya da kashi 76% bayan da ya fafata da abokin takararsa a zagaye na biyu Nabil Karoui.

An gudanar da zaben shugaban kasa a Tunusiya dai ne bayan da Allah ya yiwa shugaban kasar Beji Caid Essebsi rasuwa a karshen watan yunin da ya gabata.