A wannan lahadi ce ake sa ran al’ummar Tunusiya za su gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu.

Tashar Talabijin din Al’alam dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta ruwaito hukumar zaben kasar Tunusiya na cewa a wannan lahadi ne al’ummar kasar za su gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu, inda dan takara mai zaman kanta Kaïs Saïed zai fafata da takwaransa na jam’iyar Qalbu-Tunus Nabil Karoui.

Hukumar Zaben ta Tunusiya ta bukaci al’ummar kasar da su fito kwansu da kwalkwatarsu domin sauke nauyin dan kasa.

A ranar juma’ar da ta gabata ce al’ummar kasar Tunusiya dake zaune a kasashen Ketare suka gudanar da nasu zaben.
Kimanin ‘yan kasar Tunusiya dake kasashen Ketare dubu 385 da 546 ne suka yi rajistan yin zabe, to saidai kimanin mutane dubu 35da 820, suka kada kuri’unsu.