Shugaban majalisar shawara na jam’iyar Annahda ta kasar Tunusiya ta sanar da sunan shugaban jam’iyar Rached Ghannouchi a matsayin dan takarar firai minista.

A yayin da yake tattaunawa da tashar talabijin ta Almadayeen ta kasar Labnon, Shugaban majalisar shawara na jam’iyar Annanhda Abdulkarim Al-harouny ya ce jam’iyar su na tattaunawa da bangarorin jam’iyun siyasar kasar domin kafa gwamnati, kuma a bangaren jam’iyarsa ta gabatar da sunan shugaban jam’iyar Rached Ghannouchi a matsayin dantakarar firai minista.

A nasa bangaren Rafiq Abdoul-salam daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar Annahda ya ce jam’iyun na adawa na tattaunawa da KalbuTunis ta madugun ‘yan adawan kasar Nabil Alkaraoui wanda ya sha kayi a zaben shugaban kasar da ya gabata.

A zaben ‘yan majalisar dokoki na baya-bayan da aka gudanar a kasar ta Tunusiya, jam’iyar Annahda ce ta fi ko wace jam’iyya samun yawon kujeru a majalisar dokokin kasar inda ta samu kujeru 52, a yayinda jam’iyar KalbuTunis ta zo na biyu da kujeru 38.