Majiyar kurdawan kasar Siriya ta sanar da cewa a daren Lahadi da ya gabata jiragen yakin kasar Turkiya sun kai hari kan tawagar 'yan jaridun kasashen waje a arewacin kasar.

A cikin wani bayani da ta fitar majiyar labarai ta kurdawa a arewacin siriya ta ce harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 9.
Kungiyar kare hakin-bil-adama ta Siriya dake da hedkwata a birnin Landon ta tabbatar da kai harin, tare da tabbatar da cewa akwai yiwuwar karuwar hasarar ruyuka, ganin cewa daga cikin wadanda harin ya ritsa da su, akwai wadanda suke cikin mawuyacin hali.

Tun a ranar larabar da ta gabata ce dakarun kasar Turkiya suka fara kai farmaki kurdawan arewacin kasar Siriya bisa da'awar yaki da ta'addanci da kuma tsarkake yankunan kan iyakar kasar da Siriya.

Hukumomin Turkiya dai na kallon mayakan kurdawa na kungiyar YPG a matsayin 'yan ta'adda, don shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya bayar da umarnin kai musu hari.