Kasar Turkiya ta tabbatar wa da Iran cewa harin data fara kaddamarwa a arewacin Syria na wani dan lokaci ne.

Ministan harkokin wajen kasar ta Turkiya ne, Mevlut Cavusoglu, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da takwaransa na Iran, Muhammad Jawad Zarif, ta wayar tarho.
A tattaunawar tasu Mista Cavusoglu, ya jaddada wa takwarnasa na Iran din cewa, zasu mutunta hurimin kasar ta Syria.

A lokacin guda kuma Mista Zarifa, ya bayyana wajabcin yaki da ta’addanci a Syria, domin samar da tsaro a kasar ta Syria amma a cewarsa kamata ya yi kasashen na Syria da Turkiya su yi amfani da yarjejeniyar Adana domin magance sabanin dake tsakaninsu.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da majiyoyi daga arewacin Syria ke cewa sojojin na Turkiya sun fara kaddamar da farmaki kan kungiyar kurdawan Syria ta YPG, da mahukuntan na Turkiyya ke zarginsu da ayyukan ta’addanci masu nasaba da kungiyar PKK.

Kafin hakan dai MDD, ta bayyana matukar damuwarta akan abinda ta kira ba ta tsmmanin zai haifar da da, mai ido ba, amma ta ce tana tattaunawa da dukkan bangarorin da batun ya shafa domin gudanar da ayyukan jin kai a yankin.