Kasar

Gwamnatin kasar Turkiyya ta sha alwashin ci gaba da kutsawa cikin arewacin kasar Syriya don share mayakan kungiyar kurdawa ta YGP daga yankunan da suke iko da su a kasar ta Siriya, duk tare da kiraye-kirayen da kasashen duniya suke mata na ta janye daga kasar ta Siriya.

Shugaban kasar ta Turkiya Rajab Tayyeed Erdogan ya ce dole ne sai ya samar da tsaro a wasu yankuna na arewacin kasar ta Siriya inda zai sake tsugunar da yan gudun hijirar kasar kimani miliyon 4 da suke cikin kasar Turkiyya a halin yanzu.

Sai dai kungiyar tarayyar Turai ta bayyana damuwarta da wannan shirin na gwamnatin kasar Turkiya, saboda yi yuwar yan gudun hijiran da basa son komawa cikin kasar Siriya zasu yi kokarin yin hijira zuwa kasashen na turai.

A nata bangaren gwamnatin kasar Rasha ta yi kira ga kurdawan kasar Siriya na kungiyar YPG su shiga tattaunawa kai tsaye da gwamnatin kasar Siriya don samar da hanyar warware halin da suka fada ciki.

Kungiyar kurdawan kasar Siriya ta YPG dai tana samun taimakon kasar Amurka a kokarin da take yi na ballewa daga kasar tare da taimakon kasashen yamma, amma a cikin yan kwanakin da suka gabata Amurka ta janye sojojinta daga kasar ta Siriya, inda ta bar kurdawa cikin fargaba na shiga yaki da sojojin kasar Siriya a bangare guda ko kuma da sojojin kasar Turkiya a dayan bangaren.