Siriya : Bangarori Na Zargin Juna Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta

-KADUNA PRESS.
Gwamnatin Turkiyya da Kurdawa a arewacin Siriya, na zargin juna da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma a shiga tsakanin Amurka.

A ranar 22 ga watan Oktoban nan ne wa’adin da Turkiyya ta baiwa mayakan Kurdawa na su janye daga yankin data kira na tsaro a iyakarta da Siriya ke kawo karshe.

A yayin da Kurdawan ke zargin Turkiyya da kai masu hare hare, ta sama, da kasa, ita kuwa Turkiyyar na mai da zargin Kurdawan da kai mata jerin hare haren rokoki da manyan makamai 14 a cikin sa’o’I 36.

A halin da ake ciki dai shugaban kasar ta Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya ce zai kaddamar da hare hare da yammacin ranar 22 ga wata, idan dai har mayakan Kurdawan suka ci gaba da kasancewa a yankin.
-J.S.A
-KNPRSCD 06.
-Kaduna Press.