A cikin wani rahoton da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ta bayyana cewa adadin mutanen da rikici ya raba da muhallansu a Burkina Faso ya karu matuka.

Rahoton ya ce ya zuwa yanzu adadin mutanen ya kai rabin miliyan, daga watanni uku da suka gabata ya zuwa yanzu, kuma adadin na ci gaba da karuwa.
Haka nan kuma rahoton ya yi ishara da cewa, baya ga wadanda suka kaurace wa muhallansu a cikin gida, akwai kuma mutane kimanin dubu 16 da suka tsere zuwa kasashe makwabta domin kauce wa rikicin da aka fama da shiayankunansu, sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi.

Rahoton na hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya da aka fitar a jiya Juma’a, na zuwa ne bayan wani rahoton da gwamnatin kasar Burkina Faso ta fitar da ke cewa adadin wadanda rikicin ya raba da muhallansu ya kai mutane dubu 300 ne a kasar.