Mai Bawa Jagoran juyin juya halin musulinci na Irankan harakokin kasa da kasa Dakta Ali Akbar Velayati ya ce tushen siyasar Iran shi ne goyon baya da taimakawa al’ummar Siriya don haka ya zama wajibi mu ci gaba da aiki da gwamnatin kasar har zuwa lokacin da za a kawo karshen ‘yan ta ‘adda da masu tsatsauran ra’ayi a Siriyan.

Yayin da yake ganawa da Adnan Hasan Mahmud jakadan kasar Siriya a birnin Tehren a jiya asabar, maibawa Jagoran juyin juya halin musulinci na Irankan harakokin kasa da kasa Dakta Ali Akbar Velayati ya tabbatar da karewa da kuma mutunta hurumin kasar ta Siriya tare da cewa ya zama wajibi dukkanin kabilun kasar ta Siriya a matsayin al’umma daya ta tashi tsaye domin kare kasarta.

Velayati ya kara da cewa a halin da ake ciki, kungiyoyin gwagwarmaya na kasar Siriya nada karfin da za su iya kare kasarsu.

A nasa bangare, jakadan kasar Siriya dake nan birnin Tehran Adnan Hasan Mahmud ya yabawa gwamnati da kuma al’ummar kasar Iran kan irin gudumuwar da suka bawa kasarsa tare kuma da bayar da rahoto kan abubuwan dake faruwa a kasar.

Adnan ya kuma soki matakin da kasar Turkiya ta dauka na kai hare-hare kan kasarsa tare da bayyana hakan a matsayin abinda ya sabawa dokokin kasa da kasa.