Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ambato majiyar gwamnatin kasar ta Demokradiyyar Congo na cewa jirgin na daukar kaya ne kuma da akwai wasu ma’aikatan fadar shugaban kasa a cikinsa a lokacin da ya fado.

Tun da fari an sanar da cewa jirgin saman na jigilar kaya, mai dauke da mutane 8 a cikinsa ya bace daga allon na’urar dake sa ido akan sufurin sararin samaniya
Daga cikin mutane da jirgin yake dauke da su da akwai matukin shugaban kasar Felix Tshisekedi da majana mai kula da ayykan fadar shugaban kasa da kuma wasu sojoji. 

Jirgin dai yana kan hanyarsa ne ta zowa garin goma dake gabashin kasar
An gano baraguzan jirgin saman, sai dai har yanzu ana cigaba da cigiyar mutanen da suke cikin sa. 

Dubban magoya bayan shugaban kasar nesu ka bazama kan titunan birnin Kinshasha,bayan da labarin faduwar jirgin ya watsu bisa fargabar cewa ko an shirya juyin mulki ne.