Rahotanni da kamfanin dillancin labaran NigeriaNAN ya nakalto ya tabbatar da afkuwar hakan, aranar Lahadi da ta gabata,inda yan bindiga suka dirarwa wadanann kauyukan dake karamar hukumar Igabi da ya raba sama da mutane 2000 da mahallinsu, inda wasun su ke gudun hijra a makarantar Primary ta karamar hukumar birnin Yero
Wani da ya ganewa idonsa ya bayyana cewa matsalar ta faru ne bayan da wasu yan banga suka yi yunkurin taimakawaal’ummomin yankin domin fatattakar yan bindigan da suka addabi jama’a,wannan yasa suka bayyana cewa tun da al’ummar yankin sun dauki mataki da kansu,to ba su da sauran zaman lafiya.

Rahoton ya ci gaba da cewa ‘yan gudun hijiran sun dauki matakin rufe babbar hanyar Kaduna Zaria tare da hana ababen hawa wucewa har sai mahukuntan jihar sun kawo musu dauki, kafin daga bisani limanin wani masallaci a garin ya shawo kansu da su bi doka da oda, kada su sauki dokaa hannunsu. Limamin ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta dauki matakan gaggawa wajen tallafawa wadanda lamarin ya rutsa da su da kawo karshen hare- haren.