A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a da kungiyar Middle Belt coordinator, Comrade Godwin Ekoja ya fitar a wani shiri da ta gudanar a biranen Kaduna, Legas.

Enugu, da kuma Ibadan da aka yi wa lakabi da Tour on peace and political stability a Nigeria, sun yi kira da a saki jagroan yan uwa musulmi shaikh Ibrahin Elzakzaki da kanar sambo Dasuki da Omoyele Sowere shugaban kamfanin Saharar reporters, da kuma James Abiri da Idris Dadiyata da ake tsare dasu.

Har ila yau ya kara da cewa kungiyar bata musanta cewa akwai matsaloli masu yawa a Nigeria ba da ya kamata a shwo kansu ba, da suka hada da matsalar boko haram yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da tabarbarewar Ilimi da dai sauran su.

Don haka ya zama wajibi gwamnati ta dauki mataken da suka dace wajen magance wadannan matsaloli dake neman jefa kasar cikin halin ni Ya'su , kuma ta saki dukkan wadanda take tsare da su da tuni kotu ta bad aumarnin a sakeso, amma gwamnati tayi biris da hukumcin.