Jessica Nabongo wadda iyayenta suka yi gudun hijira zuwa kasar Amurka,an haifeta a barinin Detroit dake jihar Michigan ta Amurka, kuma tana amfani da paspot din kasar Uganda da na Amurka , ta fara tafiye – tafiye ne tun tana yar shekaru 6 da haihuwa , Nabango yar shekaru 34 da haihuwa a yanzu ta kafa tarihi bayan da ta isa tsibirin sashel da ya cika adadin kasa ta 195 da ta kai ziyara a duniya.

A lokacinda ta isa tsibirin sychel tare da iyalia da abokan arziki su 50 ta yin amfani da hanyoyi sadarwa na zamani wajen aikewa da sakon godiya ga yan uwa da abokan arziki.

Ta yanke shawar ziyartar dukkan kasashen duniya ne a shekara ta 2017 bayan da ta kai ziyara kasashe 60, kuma ta ziyarci kasashen duniya 135 a cikin shekara daya da rabi.