TATTAKI A DA'IRAR KADUNA DA KEWAYE
-KADUNA PRESS.

'Yan uwa musulmi almajiran Sheikh Zakzakiy da sauran al'ummar musulmi sun gudanar da tattaki na yankin da'irar kaduna da kewaye kamar yadda suka saba gudanarwa.
Yan uwan sun hadune a birnin suleja daga yankuna daban-daban na da'irar ta kaduna, inda ya hada garin suleja, mina, bida, maraban jos, kaduna da sauransu.

Kamar yadda suka saba a tsawon kusan shekaru uku zuwa hudu suna gudanar da tattakin ne daga cikin garin suleja sai su nufi zuba kuma su rufe tattakin a muhalli.
Da wakilinmu ke zantawa da wasu mahalarta taron sun shaida masa cewa wannan karon basu fita daga cikin garin na suleja bane domin wasu dalilai wadanda bazai iya bayyanasu dukka ba, sedai yace lallai gwanatin tarayya da na jiha sunyiwa wannan tattaki mugun nufi, ta yadda suka tanaji jami'an tsaro da 'yan daba masu yawan gaske ta yadda yawansu yakai kusan dubu goma a kiyasce.
Sun faffake a cikin ciyayi da dajikan hanyar suleja zuwa kaduna road, da nufin idan muka bar garin suleja muka dauki hanyar kaduna road su bude mana wuta tako ina su ritsamu suyi mana ruwan wuta ta gaba da baya sannan 'yan sara-sukar su far mana da sara da duka, inji shi.
Majiyar mu ta shaida mana cewa muzaharar tattakin an fara ta lafiya kuma an kammalata lami-lafiya.

-Jabeer Bin Said Al'ansariy.
-KNPRSCD 06.
-Kaduna Press.