Kimanin yahudawan sahyuniya 400 suka kutsa kai a cikin masalacin quds mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran Palastine ya bayar rahoton cewa, a jiya kimanin yahudawan sahyuniya dari hudu ne suka kutsa kai a cikin masalacin quds tare da keta alfarmar masallacin.

Yahudawan dai sun shiga masallacin ne da sunan raya ranakun idin yahudawa, inda daruruwan jami’an tsaron Isra’ila ke basu kariya, domin hana falastinawa daukar matakin hana su shiga cikin masallacin.

Koa makon day a gabata ma wasu yahudawan wadanda adadinsu ya kai dari uku sun kutsa kai cikin maswallacin masallacin, inda daga makon day a gabata ya zuwa jiya, yahudawa kimanin 700 suka shiga cikin masallacin mai alfarma.

Wannan matakin dai na zuwa ne da nufin tsokanar falastinawa da sauran musulmi mazauna birnin an Quds da ma sauran musulmin duniya, wadanda suke girmama masallacin quds mai alfarma, wanda shi ne alkiblar musulmi ta farko.