Gamayyar kungiyoyin ‘yan adawa na kasar Guinea sun yi kira da a ci gaba da gudanar da zanga-zanga don tilasta wa shugaba Alpha Conde janye yunkurinsa nayi ma kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska don ci gaba da mulki.

Gamayyar Kungiyoyi na FNDC na son dakatar da yunkurin yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara wanda zai bai wa shugaba mai ci Alpha Conde damar tsayawa takara.

Shugaban mai shekaru 81 na Duniya na son neman wa'adi na uku a zaben shugaban kasarmai zuwa a shekarar 2020.

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan mutuwar wasu fararen hula biyar a arangamar tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sanda.

Sai dai a cewar jam'iyyar ta adawa mutum kusan dari ne suka rasa rayukansu a rigingimu tun bayan da shugaban ya dare mulki a shekarar 2010.

A Jumma'ar da ta gabata 'yan majalisa da ke bangaren adawa 53 sun janye daga majalisa a wani yunkuri na kin amincewa da yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska.