Yan awaren Kamaru da ke yankin da ke magana da Turancin Ingilishi, sun kaurace wa tattaunawar da hukumomi suka fara a jiya Litinin, inda suka sha alwashin ci gaba da tayar da kayar baya.

Shugaba Paul Biya na Kamarun ne da kansaya shirya taron kasa domin lalubo hanyar sulhu tsakanin gwamnati da 'yan awaren, a kokarin ganin an kawo karshen rikicin da kasar ke ciki kimanin shekaru biyu.

Su dai mazauna bangaren na Ingilishi, na zargin nuna musu wariya ne da bangaren kasar mai rinjaye na Faransanci ke yi.
A baya gwamnatin kasar ta sha afka wa mutanen da a farko suka ce suna zanga-zangar lumana, wadanda suka hada da malaman makarantu da kuma lauyoyi.

Sama da rayukan mutum dubu uku ne suka salwanta a rikicin ‘yan awaren na kasar Kamaru, yayin da wasu fiye da dubu 500 kuwa suka rasa mahalinsu.

Kasarta kamaru dai na da gundumomi goma wadanda biyu daga cikin su da suka hada da yankin arewa maso yamma mai hedikwata a Bamenda da kuma Kudu maso yamma mai hedikwata a Buea ke magana harshen Turancin inglishi.