Rahotanni sun bayyana cewa wasu yan bindiga sun kutsa kai cikin makarantar Engravers College ta masu zaman kantadake hade da maza da mata dake garin Sabo a karamar hukumar chikun ta jihar Kaduna, kuma sun yi awon gaba da mata 6 da wasu malamai guda biyu, cikinsu har da daliba yar shekara 16 da aka yi garkuwa dasu, kuma tuni aka baza jamian tsaro domin fara binciken gano inda aka tafi da yan matan da malamn makarantar guda 2, da aka yi karguwa dasu.

Anata bangaren gwamnatin jihar Kaduna ta bakin kwamishin tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fadi cewa gwmnati ta yi tir da kai harin na rashin tausayi kan yara yan makaranta da malamansu, kuma ta aike da wakilai da suka hada da jami’an tsaro zuwa makatantar domin jijintawa iyayen wadandan abin ya shafa.

Batun garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa yana neman zama ruwan dare gama duniya a jihar kaduna inda aka samu rahotanni yin garkuwa da sama da mutane 100 a sassa daban daban na jihara wannan shekarar, wanda mafiyawanci an yi garkuwa da su ne a babbar tagwayen hanyar Kaduna zuwa Abuja.