'YAN KIDINAPIN SUN TASHI KAUYUKA 17 A KADUNA...

-KADUNA PRESS.

Akalla kauyuka goma sha bakwai ne sukayi gudun hijira daga muhallansu a fadin jihar kaduna, a tsakanin juma'ar data gabata zuwa litinin, zuwa makarantar piramare ta gwamnati dake birnin yero.

Hukumar 'yan sandan jihar ta kaduna ta tabbatar da faruwar al'amarin.

Kauyukan da lamarin yafi tsananta sun hada da Sauran Giwa, Kyauro, Jura, Anguwan Gide, Dallatu, Kosau, da sauran su dukkaninsu a karamar hukar Igabi.

Daya daga cikin 'yan gudun hijirar da mafiya yawansu matane da kananan yara Fatima Muhammad ta shaidawa wakilinmu cewa suna rayuwa a gurin kamar marasa galihu,
Wani jami'in gwamnati ya ziyarce mu harya bada wasu 'yan buhunan shinkafa. Inji ta.

Se dai mai magana da yawun 'yan sandan jihar Kaduna (DSP) Yakubu sabo yace matsalar ta samo asaline daga lokacin da 'yan kungiyar sa-kai suka gano maboyar 'yan kidinapin a wadannan yankunan kuma suka kudiri aniyyar kai musu farmaki, sedai babu arziki 'yan kidinapin din suka fatattaki 'yan sa-kan.

Akalla 'yan sa-kai mutum uku sun bace, don haka ne ma Al'ummar yankunan suka bar muhallansu don gudun farmakin 'yan kidinapin din,
Hukumar 'yan sanda ta tura wasu ma'aikata a laugh man, harma wasu sun fara komawa gidajen su. Inji shi.

-J.S.A
-KNPRSCD 06.
-Kaduna Press.