‘Yan kabilar Rohingya masu gudun hijira a kasar Bangaladesh ya yi kakakusar kan yadda majalisar dinkin duniya ta nuna gazawa wajen bayar da ilimi ga ‘ya’yansu.
Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, wakilan ‘yan kabilar Rohingya masu gudun hijira yankin Kakas bazaar da ke cikin kasar Bangaladesh a karon farko sun gana da wakilan majalisar dinkin duniya, da suka ziyarci yankin.

A ganawar wakilan ‘yan kabilar ta musulmin Rohingya sun bayyana korafinsu ga majalisar dinkin duniya, kan cewa ‘ya’yansu ba su samun ilimi a wanann sansani tun daga lokacin da aka tsugunnar da su, sabanin alkawalin da majalisar dinkin duniya ta yi musu.

Khin Mawung daya ne daga cikin jagororin ‘yan kabilar ta Rohingya da suke sansanin Kakas Bazar ya bayyana wa wakilan majalisar dinkin duniya cewa, tun lokacin da aka tsugunnar da su fiye da shekaru biyu kenan, har yanzu abbu wani shiri na bayar da ilimi ga ‘ya’yansu, alhali sun baro kasarsu ne domin gudun kisan kare dangi, duk da cewa akwai matsaloli da yawa da har yanzu suke fuskanta, amma matsalar rashin ilimin ‘ya’yansu na daga cikin amnyan matsalolin da suke ci musu tuwo a kwarya.

Bisa ga tsarin da majalisar dinkin duniya ta yi, za a karantar da yaran Rohingya da aka tsugunnar a Bangaladesh ne daidai da manhajar karatu