Daruruwan mutanen yankin na Amhara ne su ka yi cincirindo a kusa da wata kotu a garin Bahir Dar suna masu yin kira ga gwamnati da ta bayyana gaskiya akan kisan da aka yi wa wasu mutane mai alaka da yunkurin juyin mulki a yankin a watan Yuni.

A wancan lokacin, an yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da wasu fandararrun sojoji da su ka yi yunkurin juyin mulki kamar yadda mahukunta a yankin suka bayyana.

Shugaban jam’iyyar National Movement of Amhara (NAMA), Desalegn Chane, ya tabbatar da cewa jami’a tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye akan masu Zanga-zangar.

Amhara shi ne yanki a arewacin kasar, wanda kuma yake dauke da sunan kabila ta biyu mafi girma a kasar ta Habasha.