Shugaban majalisar gudanarwa na kasar Yemen Mahdi al-Mashat ya kira kasar Saudiya da ta dakatar da hare-haren wuce gona da iri da take kaiwa kan al’ummar kasar da kuma kawo karshen killacewar da ta yi wa kasar.

Mai bawa Shugaban majalisar gudanarwa ta kasar Yemen shawara kan harakokin siyasa Abdul-Malik Al-Hijriya gargadi kasar Saudiya da ci gaba da kauda kai daga yin aiki da yarjejeniyar sulhu da aka cimmawa a kasar Sweden tare da tabbatar da cewa idan kasar Saudiyar ta ci gaba dsa kauda kai kan shirin na sulhu tare da ci gaba da killace kasar za ta fuskanci martani mai tsanani daga dakarun tsaron kasar ta Yemen.

Alhijri ya tabbatar da cewa a halin da ake ciki, al’ummar kasar na cikin mawuyacin hali na bukatar jin kai, sakamakon rashin man fetir a kasar, kuma yana wuya a magance matsalar matukar dai kasar Saudiya ta ci gaba da killace kasar, don haka babu wani zabi daya ragewa al’ummar kasar face ci gaba da gwagwarmaya na karya takunkumin makiya ta hanyar mayar da martani.