Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Za Ta Cigaba Da Kyautata Alakarta Da Kasashen Larabawa

Iran

Mai Magana da yawun gwamnatin Iran, Ali Rabi’i ya bayyana cewa; Iran za ta cigaba da mika hannun abota zuwa ga makwabtanta kasashen larabawa domin tabbatar da zaman lafiya
Rabi’i ya kara da cewa; Siyasar shugaba Hassan Rauhani ta ginu ne akan kulla da bunkasa alaka a tsakanin Iran da kasashen makwabta, kuma ziyarar da shugaban kasar ta Iran ya kai zuwa kasar Armenia tana a karkashin wannan manufar ce.

Danage da taron kasashen yankin Eurasia da shugaban kasar Ira ya halarta, Rabi’i ya ce; Tun a 2015 ne Iran ta kulla yarjejeniya da kungiyar domin kafa kwamitocin hadin guiwa da za su yi nazari akan huldar tattalin arziki a tsakanin bangarorin biyu

Da yake tsokaci akan abinda ya faru a kasar Iraki na Zanga-zanga, kakakin gwamnatin Iran din ya zargi wasu masu neman dagula al’amurra shiga ciki tare da aikata laifuka.

Rabi’i ya kira yi al’ummar Iran da su kasance cikin fadaka da kuma kai zuciya nesa a yayin da suke kokarin neman hakkokinsu da suke halartattu.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu