Rahotanni da ke fitowa daga birnin Harare na kasar Zimabbawe sun bayyana cewa gwamnatin kasar ta sanar da ranar 25 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu a fadin kasar domin gudanar da Zanga- zangar nuna kin jinin takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa kasar,da ta ce yanacutar da tattalin arzikin kasar sosai.

Da dama daga cikin jami’an gwmnatin kasar ciki har da shugaban kasar Emmarson Nangwagwa ne ke fuskantar takunkumin Amurka da zargin keta hakkin dan adam a lokacin zabubbukan da aka gudanar a kasar, da kuma kwace gonakin fararan fata tare da mika su ga bakaken fata yan asalin kasar.

A farkon wannan makon ne shugaban kasar ya halarci taron ranaraddua’a ta kasa wanda mai dakin shugaban kasar Auxilia Nangwagwa ta jagoranta, inda suka yi addu’oI na neman mafita daga takunkumin, da kuma neman tsari daga duk wani bala’I na dabi’a kan kasar.