Dan takarar zaben shugaban kasa zagaye na biyu a kasar Tunisia ya bayyana cewa maida hulda da Haramtacciyar kasar Isara’ila kha’inci ne ga mutanen kasar.

Shafin yanar gizo mai suna “Arabi-21” ya nakalto Qais Sa’id yana fadar haka a wata muhawara tsakanin yan takara wanda aka gudanar a wata tashar talabijin a kasar a jiya Jumma’a.

Sa’ida ya kara da cewa wadanda suka maida hulda da kasar Isra’ila wacce ta kori wata al-umma daga kasarta, sun yi laifi, don haka suma yakamata a hukuntasu.

Dangane da ziyar yahudawan Sahyoniya dauke da passport na HKI zuwa kasar Tunisia kuma, Sa’id ya ce mutanen kasar Tunisia suna hulda da yahudawa amma shi ba zai amince wa wani bayahude ya shiga kasar Tunisia da Passport na HKI ba.

A gobe Lahadi 13 ga watan Octoba ne za’a gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu a kasar Tunisia, inda Qais Sa’id dan takara mai zaman kansa, wanda kuma ya zo na farko a zaben zagaye na farko zai shiga takarar neman kujerar shugabanicin kasar da Nabil Alqarawi na jam’iyyar “Qulbu Tunis”.