Ministan harkokin wajen kasar Iran Dr. Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, Iran tana kokarin ganin ta sasanta tsakanin Kurdawan Syria, da gwamnatin Syria da kuma Turkiya.

A zantawarsa da tashar TRT a birnin Tehran, ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, gwamnatin kasarsa na kokarin ganin an cimma daidaito da fahimtar juna tsakanin gwamnatin Syria da kuma Kurdawa gami da gwamnatin Turkiya, da zimmar ganin an kawo karshen zubar da jini a arewacin Syria.

Zarif ya ci gaba da cewa, tun lokacin da gwamnatin Turkiya ta kuduri aniyar fara kaddamar da hare-hare a kan Kurdawa da ke arewacin kasar Syria, gwamnatin Iran ta nuna rashin gamsuwarta da hakan.

Ya ce, hanyar tattaunawa da samun fahimtar juna ita kadai ce hanyar warware matsalolin yankin, ba yaki ko tayar da jijiyoyin da nuna wa juna yatsa ba.

Gwamnatin kasar Iran dai tana kyakkyawar alaka da bangarorin da ke rikicin, da suka hada da gwamnatin kasar ta Syria da kuma gwamnatin Turkiya, kamar yadda take da hanyoyi na tuntuba tsakaninta da kurdawan Syria.