Ministan harkoin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, Iran tana maraba da duk sauyin siyasa daga bangaren Saudiyya, wanda zai sanya ta gane cewa ba Amurka ce abin dogaro ba.

Zarif ya bayyana hakan ne jiya a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a birnin Tehran, inda ya bayyana cewa Iran ta sha nanata cewa a shirye take ta shiga tatatunawa tare da Saudiyya da ma sauran dukkanin kasashen yankin tekun fasha, domin samun fahimtar juna da kuma yin aiki tare domin amfanin al’ummomin yankin.

A lokacin da aka tambaye shi dangane da wasu bayanai da ke cewa Saudiyya ta aike da wasiku a asirce tana neman taimakon Iran domin karshen yakin Yemen, Zarif ya bayyana Iran a koda yaushe tana maraba da duk wani sauyi da za a samu dangane da matsayar da Saudiyya take dauka kan harkokin gabas ta tsakiya.

Ya ce yana da kyau ta gane cewa sayen makamai daga Amurka ko kuma dogaro da Amurka ba shi ne mafita ba, zaman lafiya tare da sauran makwabta da kuma yin aiki tare tsakaninta da dukkanin kasashen yankin, shi ne abin da zai bata zaman lafiya da tsaro.