Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad zarif ya bayyana cewa, a kowane lokaci Iran a shirye take ta shiga tattaunawa tare da gwamnatin kasar Saudiyya, domin samun fahimtar juna tsakanin kasashen biyu kan batutuwa da dama da suka shafi yankin.

Zarif ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da tashar TRT a daren jiya a birnin Tehran, inda ya bayyana cewa; tun kafin wannan lokacin Iran ta sha aikewa da sakon neman tattaunawa tare da dukaknin kasashen yankin tekun fasha, domin warware duk wata rashin fahimta a tsakanin kasashen yankin.

Ya ce samun fahimtar juna tsakanin kasashen yankin tekun fasha shi ne babban abin da zai kawo wa yankin zaman lafiya da ci gaban al’ummominsa, da kuma tabbatar musu da tsaro, ba shigar kasashen yammacin duniya da ko jibge sojojinsu da makamansu a cikin kasashen yankin ba.

Zarif ya kara da cewa, Iran da Saudiyya kasashe ne masu muhimamnci a yankin tekun fasha da yankin gabas ta tsakiya, da ma duniyar musulmi, saboda haka samun fahimtar juna a tsakaninsu ya zama wajibi domin ci gaban al’ummomin yankin da ma al’ummar musulmi baki daya.

A yau ne ake sa ran firayi ministan kasar Pakistan Imran Khan zai iso birnin Tehran domin isar da wani sako da Saudiyya ta aiko shi da shi, wanda ake sa ran tana neman shiga tattaunawa da kasar Iran ne.