Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa an sami gagarumin ci gaba a kungiyar Eurasian Economic Union (EEU) sannan an share fagen fara harkokin kasuwanci tsakanin kasashen kungiyar.

Jaridar Tehran times ta nakalto zarif yana fadar haka a shafinsa na Tweeter, ya kuma kara da cewa kasar zata amfana da wannan shirin sosai.

An gudanar da taron EEU ne a birnin Yerevan na kasar Armenia a ranar Talatan da ta gabata, wanda shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya sami halattarsa.

Kasashen kungiyar Eurasian Economic Union (EEU) sun hada da Armenia, Belarus, Kazakhstan, Kyrgyzstan, da kuma Rasha.
A yerjejeniyar da kasashen suka cimma a taron na Yerevan dai sun hada da kai-kawon mutane, kayakin kasuwanci, khidimomi da kuma ma’aikata a kan iyakokin kasashen kungiyar ba tare da wata matsala ba.