Ministan harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Muhammad Jawad Zarif wanda ya bayyana haka ya cigaba da cewa:Siyasar Amurka ta yin gaban kai, da kuma take dokokin kasa, suna da tasiri mai girma akan al’ummar Palasdinu.

Muhammad Jawad Zarif ya cigaba da cewa; Gwamnatin Donald Trump tana da hannu a cikin dukkanin laifukan da ‘yan sahayoniya suke tafkawa akan al’ummar Palasdinu, domin kokarinta shi ne raunana da take hakkokin palasdinawa.

Muhammad Jawad Zarif wanda ya gana da kwamitin ministoci mai kula da harkokin Palasdinawa a karkashin kungiyar ‘yan ba’ruwanmu a birnin Baku na Azaerbaijan, ya ce; Taron yana da matukar muhimmanci saboda a wannan lokacin al’ummar Palasdinu suna cikin mawuyacin hali.