Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gabatar da shawarar samar da yerjejeniyar rashin tsokana da kuma shishigi tsakanin kasashen yankin Tekun farisa.

Kamfanin dillancin labaran “Iran Press” ya nakalto ministan yana fadar haka a wata bayana da ya rubuta wacce kuma jaridar Financial Times ta kasar Amurka ta buja.

Zarif ya kara da cewa samar da irin wannan yerjejeniyar zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a tsakanin kasashen yankin. Sannan zai kawo karshen shishigin da manya-manyan kasashen duniya suke yi a harkokin tsaro a yankin.

A cikin watan Satumban day a gabata ne dai shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya gabatar da wata shawara ta samar da zaman lafiya a yankin Tekun Farisa mai suna “Shirin Samar da Tsaro A mashigar ruwa ta Hurmuz” ko “Fata” a takaice.


Ministan ya kammala da cewa a karkashin wannan yarjejeniyar kasashen suna iya kafa rundunar hadin guiwa don tabbatar da tsaro a yankin.