Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya ganada mataimakiyan ministan harkokin wajen kasar Sweden na kasar Sweden Annika Soder.

Tashar talabijin ta Presstv anan Tehran ta bayyana cewa bangarorin biyu sun tattauna al-amuran kasa da kasa da rikicin gabas ta tsakiya, har ila’yau da kuma dangantakar kasar Iran da Sweden.

Labarin ya kara da cewa ministocin sun tattauna batun yerjejeniyar shirin nukliyar kasar Iran wacce aka fi sanin sa JCPOA
Banda haka Annika Soder mataikamakiyar ministan harkokin wajen kasar ta Sweeden ta gana da tokoranta na kasar Iran Abbas Araqchi inda suka tattauna dangane da dangantakar kasashen biyu.