Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif ya isa babban birnin kasar Azerbaijan ne a jiya Talata da dare, domin halartar taron share fage na ministocin harkokin wajen kasashen da suke mambobi a kungiyar ‘yan ba ruwanmu.

A ranakun 25 da 26 ga wannan watan an Oktoba ne dai birnin Baku zai karbi bakuncin taron kungiyar ‘yan ba-rumanwu, ( NAM) a takaice, wanda shi ne karo na 18.
Shugaban kasar Iran Dr.

Hassan Rauhani zai halarci zaman da shugabannin kungiyoyin mambobi na kungiyar za su yi a jibi juma’a.