Ministan harakokin wajen jamhoriyar musulinci ta Iran ya yabawa firai ministan kasar Pakistan kan kokarin da yake yi na tabbatar da sulhu a yankin tekun Fasha.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter a jiya talata, ministan harakokin wajen jamhoriyar musulinci ta Iran Muhamad Zavad Zarif ya yi ishara kan ziyarar baya-bayan da firai ministan kasar Pakistan ya kawo nan birnin Tehran da kuma yadda yake kokari na tabbatar da sulhu a yankin tekun Fasha, sannan kuma ya bukaci kasashen yankin su kasance tare da jamhoriyar musulinci ta Iran domin tabbatar da sulhu da tsaro a yankin.

Kafin hakan dai , a ranar 25 ga watan Satumbar da ya gabata, shugaban kasar Iran dakta Hasan Rouhani ya gabatar da shirin sulhu a yankin gabas ta tsakiya yayin da ya gudanar da jawabi a zauran Majalisar Dinkin Duniya.

A ranar Lahadin da ta gabata ce firai ministan kasar Pakista Imran Khan ya kawo ziyarar kwana guda a nan birnin Tehran inda ya gana da jagoran juyin juya halin musulinci Ayatollah sayyid Aliyu Khamenei da shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran Dakta Hasan Rouhani.