Ministan harkokin wajen na kasar Iran Mohammad Jawad Zarfi ya fadi hakan ne a wajen wani taro da aka gudanar a nan birnin Tehran a hira da yayi da tashar talbijin din Al-masira ta kasar Yamen, yana mai bayyana cewa ashirye yake ya zaiyarci kasar Saudiyya domin taimakawa wajen ganin an rage zaman tankiya dake tsakanin Riyadh da Tehran, idan yanayin mai kyau da ake ciki ya ci gaba da wanzuwa.

Ya ci gaba da cewa Tehran na maraba da duk waniyunkuri da zai taimaka wajen rage zaman tankiya a yankin, da kuma hada kai da sauran bangarorin da abin ya shafa wajen ganin an kawo karshen yakin kasar Yamen.

A gefe guda kuma ya fadi cewa suna ci gaba da tuntubar juna tsakaninsa da Fira ministan kaar Pakistan Imran Khangame da ci gaba da ake samu kan batun kasar Yamen. Shi dai Imran khan ya kawo ziyara birnin Tehran a farkon watannaninda ya gana da jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullahi khamina’i da kuma shugaban kasar Iran Hassan Rohani.

Zarfi ya nanata manufofin Iran kan taimakawa alummar Yamen , yana mai cewaIran a koyaushe za ta ci gaba da kasancewa tare da alummar Yamen. Ya kuma ce mun yi Imani cewa kawo karshen yakin zai taimawa alummar kasar Yamen ne a matakin farko.