Firayi ministan kasar Sudan Abdullah Hamduk ya bayyana ziyararsa a kasar Faransa da cewa ta yi armashi.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, Firayi ministan kasar Sudan Abdullah Hamduk ya bayyana ziyararsa a kasar Faransa da cewa ziyara ce ta tarihi, wadda take da babban alfanu ga kasar Sudan.

Bayan isarsa birnin Paris a ranar Litinin da ta gabata, firayi ministan kasar ta Sudan ya gana da wasu bangarori na ‘yan siyasar Sudan da suke a kasar Faransa, daga ciki kuwa har da madugun ‘yan tawayen Darfur da yake zaune a Faransa Abdulwahid Nur, dangne da yadda za su hada karfi da karfe domin yin aiki tare da kuma ciyar da kasar ta Sudan agaba.

Haka nan kuma Hamduk ya ganada shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, inda suka tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma yadda za a kara habbaka wannan alaka.

Shugaban kasar ta Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa Faransa ta bayar da Euro miliyan 60 ga kasar Sudan domin gudanar da ayyuka na ci gaban kasar, kamar yadda kuma ya yi alkawalin cewa zai yi iyakacin kokarinsa domin ganin an fitar da Sudan daga cikin jerin kasashe da Amurak take kiran su masu daukar nauyin ta’addanci, wanda hakan zai kai ga dauke mata dukkanin takunkumai.