A yau juma'a 01/11/2019, da misalin karfe bakwai (3:00pm) na rana daruruwan yan'uwa Almajiran Sayyid Zakzaky suka fito, dan jaddada kiran ga azzalumar gwamnatin Najeriya da ta gaggauta sakin jagoran harkar musulunci a najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky, da mai dakinsa Malama Zeenatuddeen, da dubban almajiran sa.


In ba manta ba, gwamnatin Shugaban Kasa buhari na tsare da malam Zakzaky ne tun harin ta'addancin da Sojojin najeriya suka kai a zaria a shekarar 12/12/2015, inda suka ka she Almajiran sa sama da dubu (1000+) da yayan sa uku, su ka kona yayar sa da ranta, da raunata shi da iyalinsa. Da rusa duk wani muhalli malakar harkar musulunci a najeriya. Da tsare feye da 1000 daga almajiran sa.

A shekar 2016 babban Kotun Kasa da ke Abuja ta wanke shi, sannan tayi umarni da a sake shi, a bashi diyya na milin hamsin a bai wa iyalinsa itama milinya hamsin, a ginamai gida a duk inda ya ke bukata a fadin kasar nan, amma hakan ya citura da ga azzalumar gwamnatin buhari.

Bayan duk wannan ta'addancin da gwamnatin buhari tayi, a sun ta kokarin sai sun kashe shi ta hanyar ciyar da shi da shayar da guba. Ga Kuma ma tsanancin rashin lafiyar da yake fama da ita, da iyalin sa. A haka su dauko daga inda suke tsare da shi a Abuja suka dawo da shi kaduna karkashin Nasiru El rufa'i, su ka fa haramtaciyar kotu wai suna tuhumar sa da kisan kai, yayin da a ka ja lokacin a na gudanar da haramtaciyar shari'a da nufin gubar da suka ciyar da shi ya yi tasiri a jikin sa.

Bayan daukar dogo lokaci a gudanar da wannan haramtaciyar shari'a, kotu ta ba da umarnin a fita da shi waje domin kulawa da lafiyarsa, yayin da gwamnatin najeriya ta yi kutsen a can kasar Indiya tare da kawayenta na kasar waje, don ganin sun cike burinsu na ganin bayan sa. Hakan bai yu ba sai suka yan ke shawara dawo da shi gida Najeriya. Suka cigaba da tsare shi ba bisa ka'ida ba.

Ga matasan ci rashin lafiya, ga Harsha-shi, a jikin sa, ga gubar da suka ciyar da shi, amma duk da haka wanna gwamnatin tayi kunnen uwar shegu da kiraye-kirayen da a ke yin a kan su sake shi.

Muzaharar da ta yi tafiya mai tsawo a ka mike hanya, in da a ka biyo ta sha tale-tale living tins, a ka kara mike wa kashe a Junction din Mangal plaza.

daura da bakin Dogo, a nan cikin garin Kaduna.

KNPRSCD 07 ✍️
Kaduna Press
30-9-2019