A jiya Laraba 21/11/19 wanda yayi daidai da 23 ga watan Rabi'ul Auwal a ka kawo karshen Mauldin Halkoki a da'irar kaduna, an kammala gasan Mauldin ne da Halqar Ameerul Mu'uminin, Mauluddin ya guduna ne a unguwar Kyauta New Millennium city Kaduna.

Babban bako mai jawabi shine Malam Fasihul Lisan, Malamin ya fara ne da yiwa Allah godiya, sannan yace koda bamu ce komai ba wannan zama da mukayi ya isar da saƙo da a ke son isar wa, san kuma a lokaci guda a na je fan tsuntsu biyu da dutse daya, saboda ko ba komai zaka ga wanda ka dade ba ka gani ba, sannan ka sada zumunci, da kara kaunar juna, sannan ya ce Mauldin Manzon Allah ya na da anfanoni da dama, ko ba komai a na ciyar wa a wajen Maulidi.

Sannan malamin ya ce a da zaka ga jama'a na ta ihu me yasa a ke Mauldin Manzon Allah, amma yanzun an wayi gari Maulidi ya cinye kowa, Kwana kwanan ma an yi biki cika shekaru da samun kuncin Najeriya, gwamnatin da mutanen gari suka kashe kudi masu yawa. Ba dan komai ba sai dan murna da da samun abin da suka kira samun yancin kai. To ina ga wanda ya yi murna da samuwar Manzon Allah (s.a.w.a).

Haka ya cigaba da jawabai masu ratsa jiki akan  falalar Ma'aiki (SAWW).in da cikin jawabinsa ya kawo kissoshi da dama, ya kawo kissa akan ranar da Ummul Mu'umina Ummu Ayman (RA) tasha bawali Ma'aiki a rashin sani, ya zama garkuwa da ga ciwon ciki a gare ta. 

Sannan ya kawo kissar Sahabin da yazo wajen Annabin Rahama, zai aurar da yarsa, mata Manzon tsira (s.a.w.a) ya bashi zufan sa a cikin kwalba ya kai wa yarsa wannan zufan na Ma'aiki (s.a.w.a) ko kadan Mijin ta ya dan shafa a hannunsa duk wanda ya gaisa dashi sai yayi kwana arbain yana kanshi.
   Bayan ya kammala jawabin ne sai Wakilin Halqar Malam Aliyu Bakin ruwa yayi ta'aliki.


Bayan nan sai Babban bako mai jawabi, tare da wakilin Halqar da rakiyar wasu yan'uwa suka gabatar da yanka cake, sai aka raba walima akayi addu'a aka tashi.


KNPRSCD 🔟
Kaduna Press
Fatima Muhammad Ahmad✍️