Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Gano Gawawwakin Mutane 23 A Hatsarin Jirgin Sama A Kasar Congo

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasar Kongo ta bakin kakakinta Joseph Makundi,ta bayyana cewa a ci gaba da binciken da suke yi na gano wadanda hatsarin jirgin sama da aka yi a kasar Congo ya shafa, ya zuwa yanzu ta gano gawawwakin mutane 23. 

Ya kuma kara da cewa wani jami’i a filin saukar jiragen saman na birnin Goma ya shaida masa cewa ba sa tsammanin a kwai wanda zai tsira da ransa daga cikin wadanda ke cikin jirgin.

Jirgin saman samfarinDornier 228yanakan hanyarsa ta zuwagarin Beni ne mai nisan kilo mita 350 da arewacin birnin Goma inda ya silalo kasa a wani wuri da gidajen mutane yake.

Jirgin da ya yi hatsarin mallakin kamfanin Busy Bee ne da ke da jirage 3 da ke zirga -zirgaa yankin, kuma an jiyo wani daga cikin injiniyoyin da ke kula dalafiyar jiragen kamfanin na Busy Bee yana fadin cewa jirgin yana fuskantar matsalar da ta shafi nau’ra. 

Ya zuwa yanzu dai babu wani karin haske game da adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu