Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Gudanar Da Muzaharar Asaki Zakzaky A Garin Kaduna....A yau 28/11/2019 yan'uwa Almajiran Sheikh Zakzaky, sun fitowa domin cigaba da yin kira ga gwamnatin  Buhari da ta gaggauta sakin jagoran harkar musulunci a najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa, wanda da take cigaba da tsarewa tsawon shekaru fiye da hudu ba tare da laifin komai ba. Sheikh Zakzaky na tsare tun bayan harin ta'addancin sojojin Najeriya karkashin gwamnatin Buhari ta yi a ranar 12/12/2015, yadda ta kashe mabiyan sa sama da dubu, ciki har da ‘ya‘yansa uku, da kona yayar sa da ranta a gaban sa, suka tsare daliban sa daruruwa.

A shekarar 2016 babban Kotun dake Abuja ta wanke shi, tace: baiyi laifin komai ba, asake shi. Gwamnatin taki.
Bayan duk wannan ta'addancin da gwamnatin buhari tayi, a sun ta kokarin sai sun kashe shi ta hanyar ciyar da shi da shayar da guba. Ga Kuma ma tsanancin rashin lafiyar da yake fama da ita, da iyalin sa. A haka su dauko daga inda suke tsare da shi a Abuja suka dawo da shi kaduna karkashin Nasiru El rufa'i, su ka fa haramtaciyar kotu wai suna tuhumar sa da kisan kai, yayin da a ka ja lokacin a na gudanar da haramtaciyar shari'a da nufin gubar da suka ciyar da shi ya yi tasiri a jikin sa.

Bayan daukar dogo lokaci a gudanar da wannan shari'a, kotu ta ba da umarnin a fita da shi waje domin kulawa da lafiyarsa, yayin da gwamnatin ta yi kutsen a can kasar Indiya tare da kawayenta na kasar waje, don ganin sun cike burinsu na ganin bayan sa. Hakan bai yu ba sai suka yan ke shawara dawo da shi gida Najeriya. Suka cigaba da tsare shi ba bisa ka'ida ba.

Yanzu haka dai Sheikh Zakzaky (H) yana fama da rashin lafiya mai tsanani, tare da iyalansa, amma wannan gwamnatin tana nuna halin ko in kula.

Muzaharar dai ta daga ne da misalin 6:00pm a dai dai a dan mani junction da ke kan titin bypass a nan garin kaduna, yayin da a kayi tafiya mai tsawo, a ka mike hanya  har zuwa masallacin Sheikh Dahiru Bauchi, daura da bakin ruwa a nan cikin garin Kaduna.

KNPRSCD 07
Kaduna Press

Post a Comment

0 Comments

Close Menu