A ranar Juma’ar data gabata 1st November, 2019, ƴan uwa na Dandalin matasa, ƙarƙashin jagorancin Sayyid Ibrahim Zakzaky(h) na yankin Zariya, suka shiga mu'utamar na tsawon kwanaki biyu, domin kwakwkwafe tunanin su matasa din da sada zumunci musamman a gwagwarmayar addini.

An fara gabatar da taron ne da yammacin ranar Juma’ar, inda bayan halartar mahalarta, aka fara da bada shawarwari tsakanin mahalarta, inda aka yiwa maudhu’in suna da 'Muryar Matasa'. Bayan wannan, sannan aka gabatar da saukar Al’ƙur'ani da addu'o'i da sauran azkar.

Wayewar garin ranar Asabar 02/11/2019; An fara ne da gabatar da maudhu’i mai taken; ‘Tasirin Mai Ilimi A Cikin Al’umma’ inda Malam Abdullahi Khamis Dandume ya gabatar. Bayan kammalawarsa, sannan Malam Kabir Ibrahim Soba, ya gabatar da jawabi akan maudhu’i mai taken; 'Nauyin Da Ya Hau Kan Matashi Wajen Sauke Haƙƙin Jagora’. Sannan Malam Taheer Ibrahim (Abu Muhammad) ya gabatar da jawabi akan maudhu’i mai suna ‘Hadaful Asas’. Sannan daga karshe Malam Junaidu Muhammad Sani Kudan,  ya gabatar da jawabi akan ‘Muhimmancin Dogaro Da Kai Ga Matashi’.

A jiya Lahadi 03/11/2019; An ɗaura ne da gabatar da wajabi akan ‘Ƴan uwantaka A Musulumci’ inda ɗan uwa Malam Husaini Zariya ya gabatar. Sannan daga bisani ɗan uwa Malam Ibrahim ya yi jawabin rufewa (a madadin Shaikh Abdulhamid Bello Zariya, wanda aka shirya shine zai gabatar da jawabin rufewar, amma sakamakon wani uzuri mai ƙarfi daya bujuro masa, ya sanya bai samu damar halarta ba). Dan uwa Malam Ibrahim, ya taɓo kowane janibi daga maudhu’an da aka gabatar tun daga farkon taron har zuwa karshe ya yi ta'aliƙi a kai.

Daga cikin abubuwan da aka gabatar a wajen akwai; Taƙaitaccen bayani daga ƴan uwan da suka sami damar halartar waƙi'ar Zariya, dangane da darasin da suka karanta. Sannan Filin mawaƙa, Wasa ƙwaƙwalwa, Display, Tamsiliyya. Sannan aka yi jawabin godiya ga mahalarta, tare da addu’ar rufewa, aka sallami ƴan uwa cikin aminci.