Da'irar kaduna karkashin Sayyid Zakzaky (H) ta gudanar  taron makon hadin kan Al'ummar musulmi a yau asabar 16/11/2019, a nan kaduna.

Taron da 'yan uwan almajiran Sheikh Zakzaky na garin kaduna suka shirya ya gudana ne a muhallin Fudiyya rimi kaduna, da misalin karfe uku da rabi (3:30pm) na rana, da wakilin yan uwa na garin kaduna Sheikh Aliyu Tirmidhiy ne ya jagoranci taron.

Akalla malamai uku ne suka batar da jawabai masu muhimmancin gaske akan al'amarin hadin kan al'ummar musulmi, malaman sunzone daga sassan bangarorin garin na kaduna.

Sayyid Jawad ne ya fa gabatar da jawabi, mai taken samuwar Manzon Allah (s.a.w.a). Inda ya kawo bayanai da ga bangarorin mazhabobi biyu (2), Shi'a da Sunnah, sannan ya kara da cewa: Ya kamata al'umma su fahimci hadin kai da ban, hadin baki da ban, malamin ya bayyana cewa in ka yadda da Annabi Muhammad (S), to dole ne kayi aiki irin na wannan Manzon. Malamin ya tabo abubuwa masu muhimmanci, game da yanayin da muke ciki da siyasar duniya. 

Sai mai jawabi na biyu Sheikh Mai hafizai in da ya gabatar da jawabi mai taken hadin Kan Musulmi, in da ya fara da a yar alqur'ani mai girma: wa'attasimu wala ta farraku, sannan malamin ya kara tabo wasu littatafai, irin su linjila da attaura in da ya kawo muhimmancin hadin kai, da yadda al'ummar musulmi suka jahilci hadin kai. Da ga karshe shehin malamin ya yi kira da al'ummar musulmi da suji tsaron Allah, su hada kai, sannan su damu da al'amarin juna. 

Sai a ka mika abun maga ga Malam Ahmad Rufa'i, in da ya fara jawabin sa da yiwa Allah godiya, sannan ya fa jawabin sa mai taken Halin da al'ummar musulmi suka shiga, Inda ya kawo dalilai Mauldin da ga littatafan sunni, sannan ya kara da cewa: tabbas a wajen mu ba mu da ibadar da ta wuce Mauldin Manzon Allah (s.a.w.a). Sai ya cigaba da bayani a kan halin da al'ummar musulmi suka shiga, malamin ya bayyana wannan lamari da, sabawa wasiyar Manzon Allah (s.a.w.a), da ya yi a ghadeer, san ya ce: a iya nazari sa bai taba ganin wani abu mai muhimmanci da Manzon Allah (s.a.w.a) ya kwashe kwana ki uku a cikin da ji ba, in ban da al'amarin ghadeer.

Sannan malamin ya tabo fannoni daban daban, game da makircin Yahudawa da halin da suka jefa al'ummar musulmi. Sannan ya kara da cewa: wannan duk yana da na saba da fandarewar al'umma daga barin Allah, da sakon Manzon Allah. A karshe Malami ya kawo, da disan Manzon Allah, cewa: idan da musulmi biyu za su rage a duniya, sai daya yayi kira da yan ya ki amsa mashi, to musulmin daya ya rage a duniya. Malamin ya ci gaba da bayani game da yadda al'umma suke murna idan an taba wani sashi da ba a kidar su daya ba,da illar haka, da halin da hakan ya haifar a yau.

Sannan a ka mika abin magana, ga Wakilin yan'uwa na garin kaduna 
Sheikh Aliyu Tirmidhiy ya gabatar da jawabin rufe taron a inda ya fara da godiya, sannan ya cigaba da bayani inda ya kawo bayani game da yadda Malam Zakzaky (H), ya assa-sa wannan muna saba ta hadin kai, da muhimmancin wahada, sannan ya cigaba ba da bayani yadda makiya musulunci suke kokarin raba kan Musulmi.