A Safiyar yau Lahadi 3/11/2019  ne, 'Yan uwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky (H) na Majalisin Jushi da ke cikin garin Zariya, suka yi aikin shara da tsaftace muhallin makwancin Mahaifiyar Jagoran Harka musulunci a najeriya Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).

Kamar yadda su ka saba suna gudanar dashi a ko wacce ranar lahadi, na ko wanne mako, a yau ma Allah ya yarda, sun yi kamar yadda suka saba, bayan sun share tare da goge tayis din wurin, sun kuma nome ciyawar dage gefen wurin,

Kabarin Mahaifiyar na Shaikh Zakzaky na cikin wani gida ne a unguwar na Jushi, a ranar 21/12/2015 Elrufa'i ya sa aka rushe gidan, bayan harin ta'addancin da sojoji suka yi a kan Jagoran, na kashe mutane sama da dubu 1000+ daga almajirai, 'ya'ya da danginsa, da rusa gidansa da duk wani muhalli mallaki harkar musulunci a najeriya.

Ya Allah kayi Rahma ga wadanda suka bada lokacin su, dan taimakon Addinin Allah.