A Yau Talata 12/11/2019 Yan'uwa Al'majiran Sayyid Zakzaky (H) Na yankin kaduna suka gabatar da Mauludin halqa na biyar,wato Halkar Sayyida Fateemah Zahara (A,S),Babban Bako A wurin Taron Shine Sayyid Fasihul Lisan Kaduna,Wanda yayi jawabi mai Girgiza Zukatan Mahalarta, sannan yayi jankune sosai akan ya Zama wajibi musan hakikanin waye Manzon Allah (s.a.a.), Saboda wasu suna tsuke tunanin su sosai akan wajan sanin waye Manzon Allah (S).


Daga nan sai wakilin yan'uwa Na Garin Kaduna Sheikh Aliyu Tirmizi
Ya gabatar da qasaitacciyar taaliki.


Tabbas Yan'uwa sunyi kokari sosai
Sannan daga bisani aka raba Abun walima ga mutanan gari da sauran mahalarta, Anyi raban turare sannan anan Take yan halkar suka biya hakkin shuhada na mutum saba'in.


Bashir Kaduna
@ kaduna press
005