A yau Asabar 09/11/2019 a ka gudanar da Mauldin Manzon Allah (s.a.w.a), na halkoki kamar yadda a ka saba duk shekara a na fara gudanar da Mauldin Halkoki ne, tin daya ga watan Rabi'ul Auwal ne, kafin ranar 17th ga watan Rabi'ul Auwal, in da ke gudanar da na da'iratul amm.

Babban bakon da ya gabatar da jawabi a wajen wannan Mauldin, Malam Sadisu Ibraheem Bako, shehen malamin ya janyo hanlin al'umma game da falalar Manzon Rahama (s.a.w.a), game da abin da ya shafi hakuri, karamci, ibadojin, da sauran su. San ya kara da cewa: Ya kamata duk wanda ya halarci wajen Maulidi a kalla ya rike daya daga cikin falalolin Manzon Allah, da ake karanto wa a wajen.


Da ga karshen malamin ya yi kira ga wannan al'ummar, game da nauyin da ya ke kan su, na hakkin Manzon Allah (s.a.w.a.) da iyalan gidansa tsarkaka.


Sai a ka mika abin magana ga Malam mudarris, in da ya yi Karin jawabi, sannan ya bayyana cewa: ya kamata mu yi anfani da wannan dama ta Maulidi, wajen koyi da dabi'u na tausayi na Manzon Allah (s.a.w.a). Da Ga karshe ya yi addu'a ga jagora..