A yau Lahadi 11th ga watan 11-2019 dai dai da 12 ga watan Rabi'ul Auwal, Dubban nin al'umma ne suka fito dan nuna murnar su, ga zagayowar ranar da a ka hafi Manzon Allah (s.a.w.a).

Tin da misalin 7:00am na safe ne al'umma musulmi, masoya Annabi (S) su ke ta tururuwa zuwa wajen Maulidin Annabi Muhammad (S.A.W.A).


Taron dai ya samu jama'a daga kowani janibi da ga sassa daban-daban musamman mabiya mazhabar darika da na Shi'a (jafariyya). An gudanar da taron ne a filin Ahmad Bello stadium dake nan garin kaduna.