Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

ANGUDANAR DA MAULUDIN MANZON ALLAH (S) A GIDAN INJINIYA YAHAYA GILIMADa yammacin yau Lahadi 27 ga watan Rabiul Auwal 1441H dandazon masoya Manzon Allah da suka hada Musulmi da Kiristoci suka hadu a gidan Engr. Yahaya Gilima a cikin garin Kaduna, don gabatar da bikin Mauludin Fiyayyen Halitta Muhammad (S) kamar yadda aka saba gabatarwa a kowace shekara.

Mauludin na bana ya samu halartar Sayyid Abdullahi Ashura, Bauchi, inda ya kamsasa muhallin da rantsattsen jawabi a kan darajojin Manzon Allah (S).

Shaikh Aliyu Tirmizi ne ya gabatar da Ta'aliki bayan jawabin na Sayyid Ashura. Daga bisani aka gabatar da Babban bakon tare da Sayyid Aliyu Bakin ruwa suka yanka alkakin Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (S) da na jikansa Imam Jafarus Sadiq (AS).

Cikin mahalartan har da Pastor Yohanna D.Y Buru, wanda ya zo gab da fara Mauludin tare da tawagarsa aka gaggaisa ya ba da uzuri ya tafi.

Bayan karanta ziyarar ManzonAllah (S), Mawaka da suka hada da Malam Abdullahi Lushi da Malam Yunusa Saminaka sun gabatar da kasidar Manzon Allah (S) da na Sayyid Zakzaky (H).

KNPRSCD 08
Kaduna press

Post a Comment

0 Comments

Close Menu