A yau asabar 2/11/2019 dai dai ga hudu ga watan rabi'u auwal a akafara gudanar da mauludin fiyayyan halitta Annabi Muhammad (s).

Kamar yadda a ka saba duk shekara in watan Rabi'ul Auwal ya kama ana fara maudidodi ne na halkoki kafin ranar 17 ga watan Rabi'ul Auwal inda za a hadu a gabatar da Maulidi na da'ira to alhamdulilah yau dai anfara da halkar Sayyid Zakzaky (H). itace halkar farko da ta fara gudanar da taron Maulidi fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu (s.a.w) a da'irar kaduna, kamar yadda sauran halkokin zasuci gaba a sauran kwana ki ma su zuwa, insha Allah.

 Wakilin yan'uwa na da'irar kaduna Malam Aliyu Tirmizi shi ne ya kasance babban bako mai jawabin, a cikin jawabin nasa ya tabo abubuwa da dama game da falalar Manzon Rahama Annabi Muhammad (S.A.W.A) da kuma yadda al'umma suka saki koyar wan Annabi.

Daga karshe shehin malamin yarufe da yima jagoranmu addu'a da mai dakin sa malama zeenatu Allah yabasu lfy yakara musu kariya ta musamman bihaqqi muhammad wa'ali muhammad